AYANZU: Wuta Ta Kona Gida a Jalingo kurmus

Daga wakili mu a Jalingo/Newspointer News

Jalingo Taraba – 2nd 2025

Wata gobara da ta tashi a cikin dare ta kone wani gida dake kan titin Jankada, unguwar Mayo Gwoi a birnin Jalingo, babban birnin Jihar Taraba.

Gobarar, wadda ta faru da sanyin safiyar Litinin, ta lalata dukiyoyi da aka kiyasta darajarsu da miliyoyin naira. Sai dai babu wanda ya rasa ransa a cikin lamarin.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa NEWSPOINTER cewa, “Mun ga hayaƙi da wuta suna tashi daga cikin gidan. Mun yi ƙoƙari mu taimaka, amma wutar ta yi ƙarfi sosai. Muna godiya ga Allah ba a rasa rai ba.”

Jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Taraba sun tabbatar da faruwar lamarin, inda suka ce saurin da jami’ansu suka kai wajen taimako ya hana wutar yaduwa zuwa wasu gidajen dake makwabtaka.

Duk da haka, mazauna gidan sun rasa matsuguninsu, yayin da hukumomin yankin ke ci gaba da bincike don gano musabbabin tashin wutar.

An kuma shawarci jama’a da su kara lura da tsaro, musamman wajen amfani da na’urorin lantarki, domin kaucewa irin wannan masifa a nan gaba.

Don samun ƙarin sabbin labarai, ku biyo mu a:
X (Twitter): @TheNewspointer
WhatsApp, Instagram, da Facebook: @TheNewspointer
📞 Tuntuɓe Mu:
✉️ Imel:
ishakudanzumi1@gmail.com
humtarosamson@gmail.com
📱 Lambar Waya:
0707 114 4444
0813 846 5350
🖋️ Editocin Yanar Gizo:
Prince Hassan Danzumi Ishaku / Humtaro S. Humtaro
© 2024 TheNewspointer.com.ng – An tanada duk haƙƙin mallaka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *