Daga Wakilinmu, Abuja
FCT Abuja – 2nd 2025

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana ranar Juma’a 6 da Litinin 9 ga watan Yuni, 2025, a matsayin ranakun hutu na Eid-ul-Adha ga daukacin al’ummar Musulmi a ƙasar.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a madadin gwamnatin tarayya a ranar Lahadi da yamma a birnin Abuja.
A cikin sanarwar, Ministan ya taya dukkan Musulmi murnar wannan babbar Sallah, yana mai kira gare su da su ci gaba da bin koyarwar Annabi Ibrahim (A.S) ta sadaukarwa, biyayya da juriya, musamman a wannan lokaci mai albarka.
Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya su yi amfani da wannan dama wajen yin addu’o’i domin zaman lafiya, hadin kai da cigaban ƙasa.

“Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta ci gaba da himma wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa,” in ji shi.
Eid-ul-Adha na daya daga cikin manyan bukukuwan Musulunci da ake gudanarwa domin tunawa da gwajin biyayya da Annabi Ibrahim ya nuna ga Allah, wanda daga bisani aka sauya da rago.
Bikin na kunshe da sallar Idi, yanka dabbobi, da rabawa talakawa da ‘yan uwa, tare da jaddada zumunci da taimakon juna.
Gwamnatin Tarayya ta yi fatan alheri, da zaman lafiya a wannan lokaci, tana kuma bukatar al’umma su zauna lafiya da juna domin dorewar ƙasar nan.

Don samun ƙarin sabbin labarai, ku biyo mu a:
X (Twitter): @TheNewspointer
WhatsApp, Instagram, da Facebook: @TheNewspointer
📞 Tuntuɓe Mu:
✉️ Imel:
ishakudanzumi1@gmail.com
humtarosamson@gmail.com
📱 Lambar Waya:
0707 114 4444
0813 846 5350
🖋️ Editocin Yanar Gizo:
Prince Hassan Danzumi Ishaku / Humtaro S. Humtaro
© 2024 TheNewspointer.com.ng – An tanada duk haƙƙin mallaka.
