Jalingo, Taraba – 4 ga Yuni, 2025

Shugaban hukumar National Youth Service Corps (NYSC) na Jihar Taraba, Mista Ella Aji Williams, ya bukaci sabbin masu kammala hidimar ƙasa da su ci gaba da nuna kishin ƙasa, da ɗa’a da kuma dogaro da kai. Ya bayyana hakan ne yayin bikin kammala hidima na Batch ‘B’ Stream 1 na shekarar 2024, da aka gudanar a faɗin jihar, ciki har da Jalingo da Ardo-Kola.
Mista Williams ya yabawa matasa masu hidimar ƙasa bisa gudunmawar da suka bayar wajen haɗin kai da cigaban al’umma, inda ya ce ayyukan da suka gudanar a cikin al’ummomi za su ci gaba da kawo tasiri a rayuwar jama’a.

Ya ja hankalin su da su guji tafiya da daddare da kuma su kasance masu lura da tsaro. Haka kuma, ya shawarce su da su yi amfani da ƙwarewar sana’o’in hannu da na dijital da suka samu a lokacin hidimar, domin su zama masu ƙirƙiro da ayyukan yi, ba masu neman aiki kawai ba.
A yayin bikin, an bai wa Mista Williams Lambar Girmamawa ta Musamman daga Mind the Gap Digital Skills Initiative, saboda irin gudunmawarsa wajen ƙarfafa ilimin fasahar zamani da ƙwarewa a tsakanin matasan NYSC a jihar Taraba. Wannan shi ne karo na farko da aka bai wa wannan lamba a matakin ƙasa baki ɗaya.

Jimillar matasa 617 ne suka kammala hidimar ƙasa, yayin da 16 daga cikinsu aka tsawaita musu shekara saboda laifuka daban-daban.
An gudanar da bikin cikin sauki bisa umarnin NYSC na ƙasa kan gudanar da biki cikin sauki da kamala.

