Daga Jummai Ishaku /Labarin Newspointer
Jalingo, Taraba – 06 ga Yuni, 2025

Gwamnan Jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas, ya bayar da gudummawar miliyoyin naira ga kungiyoyin addinin Musulunci da iyalan malaman addini 34 da suka rasu, a wani bangare na shiri don bikin Eid-el-Kabir mai zuwa.
An raba kudaden a garin Jalingo a ranar Laraba ta hannun wakilin gwamnan, Alhaji Hussaini Ismail.
Daga cikin wadanda suka amfana da tallafin akwai: Kungiyar Malaman Wa’azi ta Musulunci, Kungiyar Limaman Juma’a, Kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya (Reshen Taraba), Tijjaniya Initiative for Grassroots Mobilization, Majalisar Shari’ar Musulunci ta Najeriya (Reshen Taraba), Izala Youth Preachers, Jam’atul Islahudeen, da kuma Qadiriyya.

Iyalai da suka karɓi tallafi sun haɗa da na marigayi Malam Ishaka Bawuro, Malam Hamma Suleiman, Malam Danjuma Abubakar, da Malam Lamido Zubairu.
Gwamna Kefas ya kuma amince da biyan kudin jinya na wasu malamai da ke fama da rashin lafiya a halin yanzu.
A wajen rabon kudaden, Alhaji Ismail ya bayyana cewa wannan kyauta na cikin manufar gwamnatin Kefas na ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban-daban a jihar.
“Wannan tallafi alamar cikakken sadaukarwa ne daga Gwamna Kefas wajen tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da jin daɗin al’umma, ba tare da la’akari da bambancin addini ba,” in ji shi.

Shugabannin kungiyoyin da suka amfana sun bayyana godiyarsu, suna mai cewa wannan taimako ya kawo sauƙi da farin ciki ga iyalai kafin bikin Sallah.
An yabawa wannan mataki a matsayin wani ci gaba na musamman wajen kyautata dangantaka tsakanin gwamnati da al’ummar Musulmai a jihar.

