Daga Sam Kutos | Abuja | Lahadi, 8 ga Yuni, 2025

Tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Yakubu Gowon (rtd), ya bayyana Yaƙin Basasa na Najeriya da aka yi daga 1967 zuwa 1970 a matsayin lokaci mafi wuya a rayuwarsa, yana mai cewa wannan yaƙi ba don kiyayya aka yi shi ba, sai don ceto dunkulalliyar ƙasa.
Janar Gowon, wanda ya jagoranci Najeriya a lokacin yaƙin na tsawon watanni 30, ya bayyana haka ne a babban taron ƙungiyar Fellowship na Maza Kiristoci na cocin Anglican na Abuja, inda aka karrama shi da lambar yabo ta Lifetime Integrity and Achievement a ranar Asabar.
Da yake jawabi a taron, tsohon shugaban ƙasar ya ce, ko da yake yaƙin ya kasance mai zafi da raɗaɗi, ya zama dole don ceto ƙasar daga rarrabuwar kawuna.

“Ina tunawa da yaƙin basasa. Shi ne mafi wahala a rayuwata,” in ji shi. “Ba ni na zaɓi hakan ba, amma dole ne na jagoranci ƙasar domin a ci gaba da kasancewa ƙasa ɗaya. Ba don kiyayya ga wani yanki ba ne, ina tabbatar muku.”
Gowon, wanda ya cika shekara 90 a bara, ya bayyana irin yadda ya dogara da addu’a da imani wajen yanke shawara a lokacin mulkinsa. A cewarsa:
“Duk abin da nake yi, ina yin addu’a ga Allah don ya nuna min abin da ya dace in yi, bisa kauna da girmama mutane gaba ɗaya.”
Ya sake jaddada kalmar da aka fi saninsa da ita bayan yaƙin: “Babu nasara, babu shan kashi”, yana kira da a rungumi yafiya, hadin kai da zaman lafiya a tsakanin dukkan ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da kabila ko addini ba.

Gowon ya kuma ja hankalin shugabanni da al’umma gaba ɗaya su ci gaba da aiki don zaman lafiya da fahimtar juna, yana mai cewa ɗaukakar Najeriya na cikin haɗin kanta.
Yaƙin basasa, wanda ya barke sakamakon sanarwar ballewar Biafra daga Najeriya, yana daga cikin abubuwan da suka fi ƙayatar da tarihin ƙasar. Gowon, wanda a lokacin bai wuce shekara 32 ba, ne ya jagoranci Najeriya a lokacin yaƙin kuma ya ƙaddamar da shirin sake farfaɗowa da aka fi sani da Three Rs: Reconciliation (Sasantawa), Reconstruction (Sake Gina), and Rehabilitation (Sake Farfaɗo da rayuwa).
Jawabinsa ya zo ne a daidai lokacin da ake sake kira da a gudanar da zaman tattaunawa da gina ƙasa, musamman ganin yadda matsalolin tsaro da rarrabuwar kai ke ci gaba da addabar wasu sassan Najeriya.

