Ranar Dimokuraɗiyya: Tsohon Ɗan Takarar Gwamna na YPP a Taraba ya Yabi Tinubu da Kefas kan Ci gaban Mulki

Daga Wakilinmu

Jalingo Taraba – 12 ga Yuni, 2025

Tsohon ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar Young Progressives Party (YPP) a jihar Taraba, Sa’ad Hassan Abubakar, ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, bisa abin da ya bayyana a matsayin ci gaban da suke samu a harkar mulki da raya ƙasa.

Abubakar, wanda kuma ya tsaya takarar Sanata na Taraba ta Arewa a zaɓen 2023, ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Jalingo yayin hira da manema labarai a wani ɓangare na bikin Ranar Dimokuraɗiyya ta bana.

Ya jinjina wa gwamnatin Tinubu bisa irin kokarinta na dawo da kwarin gwiwa da daidaita tattalin arziki tare da farfaɗo da manyan cibiyoyin ƙasa, yana mai cewa wasu daga cikin manufofinsa sun fara haifar da ɗa mai ido.

“Gwamnatin na aiki a hankali domin dawo da kwarin gwiwa, daidaita tattalin arziki da kuma gina tubalin ci gaba mai dorewa a Najeriya,” in ji shi.

Ya ce duk da ƙalubale, Najeriya ta samu ci gaba mai ma’ana a tafarkin dimokuraɗiyya tun daga 1999 zuwa yau.

Game da halin da ake ciki a Taraba, Abubakar ya yaba da salon jagoranci na Gwamna Kefas, yana mai cewa an samu inganta tsaro da ƙaruwar yarda da gwamnati a tsakanin al’umma.

“Tsarin tsaronmu ya inganta sosai. Ya kamata matasa su haɗa kai su ba Gwamna Agbu Kefas goyon bayan da zai taimaka masa ya cimma nasara,” in ji shi.

Tsohon ɗan siyasar ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da jajircewa wajen kare dimokuraɗiyya da kuma bayar da goyon baya ga shugabanni a duk matakan gwamnati domin ci gaban ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *